Hatsarin jirgin sama a Belarus

Hatsarin jirgin sama a Belarus

Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani jirgin saman soji a Belarus.

Sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Tsaro ta Belarus ta bayyana cewa, jirgin saman sojin samfurin Yak-130 ya fado dauke da matuka 2 a lokacin da yake bayar da horo a yankin Brest na kusa da garin Baranovichi, kuma ya fado jim kadan bayan tashinsa saboda matsala da injinsa ya samu.

Mutanen dake cikin jirgin 2 sun rasa rayukansu.

Sanarwar ta kuma ce, sakamakon kokarin da matukin ya yi, ya sanya jirgin ba fado a kan gidajen mutane ba, kuma duk da mutanen sun yi amfani da lema amma hakan bai kubutar da rayuwakansu ba.

Kwamitin Bincike na Belarus ya fara gudanar da binciken gano musabbabin hatsarin.

 


News Source:   ()