Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a jihar California ta Amurka.
Hatsarin ya afku a gabar garin Point Loma na San Diego inda jami'an tsaron tekun Amurka suka kai dauki wajen.
Ana tunanin jirgin na dauke da 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba kuma an kubutar da wasu mutanen 23 da aka kai asibiti.
An fara gudanar da bincike game da hatsarin.