Mutane 36 sun rasa rayukansu wasu 60 sun jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa a yankin Hualien na kasar Taiwan.
Bayanan da jaridun Taiwan suka rawaito daga Ma'aikatar Sufuri na cewa, jirgin kasan mai tarago 8 kuma dauke da mutane kusan 350 ya sauka daga layin dogo a lokacin da ya shiga wata hanyar karkashin kasa.
Tarago na 4 da na 5 na jirgin sun samu babbar matsala, an kuma tura ma'aikatan kwana-kwana da na ceto zuwa wajen.
Mutane 36 ne aka tabbatar sun mutu yayinda wasu 60 suka samu raunuka a hatsarin.
Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ta sanya an fara bincike game da ibtila'in.