Hatsaniya ta ɓarke a zauren taron yanayi na COP29 da ke gudana a Azerbaijan

Hatsaniya ta ɓarke a zauren taron yanayi na COP29 da ke gudana a Azerbaijan

Bayanai sun ce tattaunawa kan yadda za’a tunkari shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump game da batun sauyin yanayi da irin matakan da zai dauka, shine abinda kowacce kasa ke da ra’ayin ganin an tattauna.

Bayan bude taron shugaban hukumar kula da sauyin yanayi Simon Stiell ya shaidawa kasashe cewa yanzu lokacine da za’a nunawa duniya cewa ba kasa daya ce ke da ikon samar da mafita a fannin sauyin yanayi ba.

Simon ya ce a yanzu ba lokaci bane na nuna raki kan wani shugaba ba, kamata yayi a hada kai wajen samar da mafita daya kwakwara a wani abu mai kama da sarkin yawa yafi sarkin karfi.

Yaki da sauyin yanayi a duniya yanzu haka shine babbar matsalar da kowaccce kasa ke  fuskanta, a yayin da ake ganin nasarar Donald Trump zata iya zama cikas ga yakin da kuma irin kudaden da Amurka ke kashewa wajen yaki da cutar.

Bayanai sun ce bayan kammala yamutsa gashin baki da kuma nuna juna da yatsa kan batutuwan da za’a tattauna taron ya dora daga inda aka tsaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)