Hasken nasara a Libiya

Hasken nasara a Libiya

A kasar Libiya inda aka kwashe shekaru ana tafka rikici an fara samun haske a karon farko, ayayinda lamurka suka fara goyon bayan Halattaciyar Gwamnatin Kasar, mayakan Janar Hafter kuma sun fara janyewa daga yammacin Libiya da kuma daga wasu yankunan kasar da dama.             

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal. Can ACUN manazarci akan harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arzikin da Hallayar Dan Adam watau SETA....

Babban dalilin da ya haifar da wannan nasarar da aka fara samu a Libiya shi ne goyon bayan da gwamnatin kasar ta samu daga kasar Turkiyya. Hadaka da aikin horarwa da sojojin Turkiyya suka yi da sojojin gwamnatin Libiya  da sansanonin da suka kafa a Tripoli da Misrata sun baiwa gwamnatin kasar damar kare sararin samaniyarta.

Mayakan Janar Hafter wadanda kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Misira, Faransa da Rasha ke goyawa baya sun yi nasarar karbe ikon wasu yankunan Libiya inda suka yi yunkurin karbe ikon Tripoli. Ita kuwa Turkiyya ta hanyar siyasa d soji ta fara goyawa gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa bayan juyin juhani a shekarar 2011.

Turkiyya ta fahimci cewa idan har bata dauki matakai ba za’a iya kafa mulkin kama karya a Libiya kamar yadda aka kafa a Misira. Hakan ne ya sanyata daukar matakan da suka dace na kare muradun kanta da kuma na kasar ta Libiya.

Bayan yarjejeniyar da aka yi da gwamnatin Libiya ne aka bude sansanin soji a Tripoli da Mistura tare da hadin kan sojojin kasar masu goyon bayan gwamnati. Ta horarwa da taimakawar da Turkiyya ta basu ne suka yi nasarar karbe ikon sararin samaniyya daga hannun mayakan Hafter. Haka kuma jirgin yaki mara matuki kirar TB2 da Turkiyya ta samawa gwamnatin kasar ya kara mata karfin gwiwar kalubalantar mayakan Janar Hafter.

Turkiyya dai ta yi amfani da dabarunta na yaki da kungiyar ta’addar PKK, da kuma magance rikicin Siriya a Libiya. Akan haka ne jiragen yaki marasa matukan da Turkiyya ta samawa gwamnatin kasar suka yi nasarar lalata na kirar Rasha masu samfarin Panstir da kuma ruguza shirin taimakawa mayakan da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi.

Ta hanyar taimakawa dakarun gwamnatin kasar ne suka yi nasarar karbe ikon yammacin Libiya har izuwa iyakokin Tunisia da kuma mallakar ikon sansanin sararin samaniyar Vatiyye. A yayinda dakarun Hafter ke cigaba da rasa yankuna ne dakarun gwamnatin kasar ke yunkurin kara daukar matakan karbe ikon muhimman garuruwa da suka hada da Tarhuna da Sirte.

Haka kuma ayayinda kasashen dake goyawa mayakan Janar Hafter baya kaman su Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa suka fara ganin matakan soja ba zasu haifar da da mai ido ba suka fara kira da a dauki matakan siyasa ne, ake ganin cewa dakarun gwamnatin kasar Libiya ke kara mayar da himma domin karbe ikon wasu muhimman garuruwan kasar.

 

Wannan sharhin Mal. Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayyar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya.


News Source:   www.trt.net.tr