Yayin tattaunawa da ita a kafar yaɗa labarai ta CNN Harris ta yi batutuwa da suka hadar da salon da za ta yi amfani da shi wajen ci gaba dai bai wa Isra’ila makamai yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da wakana.
Kamala ta kuma ce batun kare iyakar ƙasa da kuma takaita kwararar baƙin haure musamman ta kudancin ƙasar har yanzu abu ne da ke cikin tsare-tsare da manufofinta don haka sam ba za ta yi wasa da shi ba.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren bayanin Kamala Harris
Ta ce za ta ci gaba da amfani da ƴan majalisar da ke goyon bayanta, har sai ta cimma burinta na tabbatar da dokar bakin hauren, abin da zai ba ta damar cimma muradinta cikin sauki.
Game da batun bai wa Isra’ila makamai kuwa, Kamala ta ce ba ta da wani haufi kan yadda Joe Biden ke bai wa ƙasar makamai, amma da zarar ta zama shugaba za ta bibiyi tsarin bada makaman la’akari da yadda Isra’ilar ke kashe fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba.
Ni da Joe Biden ƙarkashin gwamnatinmu mun yi aiki da majalisar dokoki kan batun kwararar bakin haure, lamarin da ke da matukar muhimmanci ga Amurkawa, ƙarkashin wannan mun yi aiki wajen samar da wata sabuwar doka wadda ni na goyi bayanta, amma saboda keta irinta Donald Trump, haka ya yi amfani da ƴan majalisar da ke goyon bayansa suka daƙile wannan doka duk kuwa da yadda za ta taimaka wajen tsare iyakokinmu kawai don biyan bukatarsa ta siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI