Harris ta kammala neman da ta ke na mataimaki bayan da ta gana da wasu manyan ƴan takara 3, wato gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz, sai sanata mai wakiltar jihar Arizona, Mark Kelly da gwamnan Pennsylvania, Josh Shapiro kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
Makwanni biyu da suka wuce ne kawai Harris ta fara neman mataimaki, jim kaɗan bayan da shugaba Joe Bidn ya janye daga takarar shugabancin ƙasar, ya kuma zaɓe ta ta maye gurbinsa.
Zaɓen abokin takara na daga cikin matakan da za su fi yin tasiri a a harkar siyasarta, a yayin da ta ke hanzari wajen fara yaaƙin neman zaɓe ddon ƙalubalantar tsohon sshugaba Trump a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Ilahirin mutanen da Harris za ta zaɓe mataimaki daga cikinsu fararen fata ne, waɗanda su ke da tarihin lashe zaɓe a inda fararen fata suka mamaye, da kuma masu zaɓe da ba su da jam’iyya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI