Harris da Biden sun taya Trump murnar nasarar da ya samu

Harris da Biden sun taya Trump murnar nasarar da ya samu

Kafofin yada labaran Amurka cikin su harda CBS sun ce Harris ta bukaci shirin mika mulki cikin kwanciyar hankali da lumana tare da bukatar zababen shugaban ya zaman shugaban kasa ga kowane BaAmurke.

Ofishin yakin neman zaben Trump ya ce shugabannin biyu sun tattauna muhimmancin hada kan Amurkawa lokacin tattaunawar ta su ta waya.

Rahotanni sun ce lokacin tattaunawar Trump ya jinjinawa Harris saboda kwarewarta da kuma jajircewarta lokacin da aka dauka ana yakin neman zabe.

Lokacin yakin neman zaben Trump ya dinga kiran Harris makaryaciya da kuma mara hankali, ya yin da ita kuma take bayyana shi a matsayin wanda ke sanya kansa a gaba kawai, maimakon jama'a.

Shi ma shugaban kasa Joe Biden ya kira Trump ta waya domin taya shi murnar nasarar da ya samu, kamar yadad fadar White House ta tabbatar.

Sanarwar fadar ta ce Biden ya jaddada aniyarsa ta ganin an kammala shirin mika mulki cikin kwanciyar hankali, tare da gayyatar Trump da ya same shi a fadar shugaban kasa.

Gobe ake saran shugaba Trump ya yi jawabi ga Amurkawa a kan sakamakon zaben.

Fadar White House ta kuma ce Biden ya yi magana da Harris inda ya jinjina mata saboda rawar da ta taka wajen yakin neman zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)