Harin ta'addancin da ka kai da bama bamai sau biyu jeri ga juna a kudancin jihar Kandahar dake kasar Afghanistan ya yi sanadiyar rayukan farar hula 15.
Mai magana da yawun Walin Kandahar Bahir Ahmadi ya shaidawa manema labarai da cewa bama-bamai biyu da aka ajiye a gefen hanayn garin Spin Buldak dake jihar Kandahar sun tashi yayin da motocin farar hula ke wucewa.
Lamarin ya haifar da rasuwar rayukan farar hula 13 a cikin wata motar farar hula da suka hada da yara uku inji Ahmadi. Haka kuma wasu uku sun raunana. Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin akan kowa ba.
Haka kuma a yayinda da bam-baman suka tashi yari yaro tare da mahiafimnsa suna wucewa lamarin da yayi sanadiyar rayukansu.