Harin ta'addanci ya kashe mutum 10 a New Orleans na kasar Amurka

Harin ta'addanci ya kashe mutum 10 a New Orleans na kasar Amurka

Rundunar 'yan sandan yankin ta ce mutumin da ya aikata aika-aikar, ya yi nufin kutsawa cikin dandazon jama'a ne, tare da harbin kan mai 'uwa dawabi.

Bayanai sun ce, mutane 30 suka samu munanan raunuka, wadanda a halin yanzu ke karbar kulawar likitoci a asibiti.

Magajin garin na New Orleans, LaToya Cantrell ya bayyana wannan al’amari a matsayin wani hari na ta’addanci kan mutanen da ba su ji ba su gani ba, yayin da su ke tsaka da gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara.

Tuni hukumar tsaro ta FBI ta kaddamar da bincike, kamar yadda wani babban jami’in hukumar Alethea Duncan ya shaidawa manema labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)