An sanar da cewa rushewar wani ginan gidan gwamnati sakamakon hari bam da aka kai da mota a garin Jorinto dake karkashin gundumar Jauja a kudu maso yammacin Colombia ya yi sanadiyar rayukan mutane 17.
Jami'an gwamnatin sun bayyana lamarin a matsayin harin ta'addanci. tuni dai an garzaya da wadanda suka raunana asibiti domin yi musu jinya.
Sabili da karfin harin ya lalata gidaje da wasu kadarori dake kusa da inda aka kai harin.
Shugaban kasar Ivan Duque ya yada a twitter inda yake tir da Allah wadai da kai harin, ta'addanci ya kasance makamin matsorata, na bayar da umarni ga jami'an tsaro dasu gano wadanda suka aikata laifin. Ala kulli halin zamu ci gaba da yaki da ta'addanci"