Mutane 4 sun samu raunuka sakamakon harin ta'addanci da aka kai da mota dauke da bam a yanlin Afrin na arewacin Siriya.
An tayar da motar da aka dasawa bam a tsakiyar gundumar Afrin da aka raba da 'yan ta'adda a karkashin Farmakan Reshen Zaitun.
Rahotanni sun ce mutane 4 ne suka jikkata sakamakon harin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewar 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suka kai harin amma saboda sun jikkata fararen hula ya sanya suka ki daukar alhakin kai shi.