Harin Rasha ya kashe ɗaliban kwalejin Sojin Ukraine 41 a Poltava

Harin Rasha ya kashe ɗaliban kwalejin Sojin Ukraine 41 a Poltava

Da sanyin Safiyar jiya Litinin ne, Rasha ta ƙaddamar da harin da wasu makamai masu linzami guda biyu wanda ya shafi gine-ginen asibiti da na kwalejin horar da Sojoji a birnin Poltava mai tazarar kilomita 300 daga birnin Kyiv fadar gwamnatin Ukraine, yankin da ke ɗauke da mutane akalla dubu 300.

Tuni dai wannan hari na Rasha ya haddasa kakkausar suka ga gwamnatin Ukraine daga ƴan ƙasar a shafukan sada zumunta, bayanda suka ɗora alhakin asarar rayukan ɗaliban Sojin kan mahukunta waɗanda suka sahale gudanar da taron duk da barazanar hare-haren Rasha a yankin.

Shugaba Zelensky a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta bayan faruwar harin, ya sanar da bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan yadda harin ya faru dama sakacin da ya kai ga asarar rayukan.

A cewar shugaba Zelensky fiye da mutane 180 ne suka jikkata a farmakin na Rasha, abin takaici har da mutane 41 da harin ya kashe bayan ya rusa babban gini a kwalejin horas da Sojojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)