Sanarwar da ofishin Firaministan na Birtaniya Keir Starmer ya fitar a yau Laraba, ta bayyana cewa hare-haren da Rashan ke ci gaba da kaiwa tashar jiragen ruwa ta Ukraine da kuma kan jiragen da ke aikin dakon hatsin ƙasar a tekun Black Sea ba kaɗai Falasɗinu ba, ya dakatar da shirin isar da hatsi ga ilahirin yankin kudancin duniya da suka ƙunshi nahiyar Africa da Latin Amurka da Caribbean baya ga wani yanki na Asia da kuma Oceania.
Sanarwar ta ruwaito Stermer na cewa, shugaba Vladimir Putin na Rasha na son ɗaukar aradu da ka dangane da batun wadata duniya da abinci duk dai a yunƙurinsa na ganin ya tilastawa Ukraine miƙa wuya, wannan dalili ya sanya shi tsananta hare-hare kan jiragen na Kiev da ke aikin kai hatsi sassan duniya.
Ko Litinin ɗin da ta gabata, sai da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana yadda hare-haren na Rasha ya shafi jiragen fararen hula aƙalla 6 baya ga lalata tarin abincin da aka nufaci kaisu ga wasu yankuna ciki har da yankin Falasɗinu mai fama da yaƙi.
Ofishin Firaministan na Birtaniya ya ce daga ranar 5 zuwa 14 ga watan Oktoban da muke Rasha ta lalata jiragen dakon abinci aƙalla 4 batun da Starmer ke cewa hare-haren sun hana isar da abinci ga miliyoyin mutanen da ke tsananin buƙatar abincin, laifin da kai tsaye Firaministan ya ɗora kan Putin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI