An sanar da cewa harin bam din da aka kai a Cibiyar Ilimin Kevser Danish dake Kabul ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane goma.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan Tarık Aryen, ya shaidawa manema labarai da cewa an kai harin bam a Cibiyar Ilimin Kenver Danish dake yankin Dasht-i Barci a Kabul.
Aryen, ya kara da cewa a binciken farko mutane 10 suka rasa rayukansu sakamakon harin, inda kuma wasu 20 suka jikkata.
Wadnda lamarin ya faru akan idonsu sun bayyana cewar yawan wadanda suka mutum sun fi hakan kuma hari ne na kunar bakin wake.
Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin akan kowa ba.