Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce mutane 15 ne suka mutu sannan wasu 83 suka jikkata a wurare da dama da ke kudancin kasar, sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan 'yan kasar a lokacin da suke kokarin shiga garuruwansu da aka mamaye.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Labanon kuma shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kudancin kasar ya ce har yanzu ba a kai ga wani yanayi ba na komawar wadanda suka tserewa rikici a Lebanon kauyukansu, musamman wadanda ke kusa da kan iyaka.
Kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya bukaci da a dauki mataki kan Isra'ila yayin da sojojin kasar suka bude wuta kan fararen hula, inda suka kashe akalla mutane hudu ciki har da wani sojan Lebanon daya tare da jikkata sama da mutum 40.
Shima shugaba Joseph Aoun ya yi Allah wadai da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta yi, inda ta yi alkawarin janye dakarunta daga kudancin Lebanon a yau Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun bude wuta kan wata motar soji tare da raunata wani sojan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI