Harin Isra'ila ya hallaka Falasɗinawa 40 a tudun mun tsira da ke al-Mawasi

Harin Isra'ila ya hallaka Falasɗinawa 40 a tudun mun tsira da ke al-Mawasi

Sojin na Isra’ila waɗanda su da kansu suka amince da sansanin na al-Mawasi a matsayin tudun mun tsira tun farkon faro yaƙin na watanni 11, a cewarsu sun ƙaddamar da harin ne bayan gano wata cibiyar bayar da umarnin kai musu hari da Hamas ke gudanarwa a cikin sansanin.

Fiye da mutane 60 suka jikkata a harin na safiyar yau Talata, bayan wasu 40 da suka mutu, lamarin da ya mayar da jumullar Falasɗinawan da Isra’ilan ta kashe zuwa dubu 41 da 20 baya ga wasu fiye da dubu 90 da ta jikkata daga faro yaƙin kawo yanzu.

Tuni dai Hamas ta yi watsi da iƙirarin Isra’ila na cewa ta ga guda cikin mayaƙanta a gab da sansanin lamarin da ya kai ta ga ƙaddamar da hare-haren na yau da safe.

Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant wanda ke goyon bayan tattaunawar sulhu da Hamas don samun damar kuɓutar da fursunoninsu da ke hannun mayaƙan ƙungiyar, ya ce makamantan hare-haren da za su hana Hamas iya tasiri a kudancin Gaza su ne za su basu damar iya karɓe iko da dukkanin ɓangarorin yankin tare da takure mayaƙan waje guda.

Wasu bayanai na nuna har zuwa yanzu akwai sauran fursunonin Isra’ila 100 a hannun Hamas cikin fiye da 250 da suka kwashe ranar 7 ga watan Oktoban bara ko da ya ke akwai fargabar da dama daga cikinsu sun mace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)