An sanar da cewa sakamakon harin da aka kai a Kabul babban birnin Afghanistan mutum 10 sun rasa rayukansu.
Mataimakin shugaban kasar Emrullah Salih ya bayyana cewa a yankin Vazir Akber an kai harin da ya yi sanadiyar raunanan mutane 51.
Kamar yadda kafar yada labaran ToloNews ta rawaito, Salih ya yi alkawarin za'a gudanar da bincike akan lamarin.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan kasar Afghanistan Tarik Aryan ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun ajiye rokokin a cikin wata babbar motar tirela.
Daga cikin rokoki 23 da aka harba Kabul daya ya fada ofishin jakadancin Iran dake birnin lamarin da ya lalata jikin ginar da dama.
Kungiyar Taliban ta yi watsi da ikirarin cewa ita ta kai harin.