An sanar da hallakar mutane hudu a harin bam da aka kai a jihar Gazne dake kasar Afghanistan.
Mai magana da yawun Gazne Wahidullah Jumazada ya shaidawa manema labarai cewa, tashin bam da aka ajiye gefen hanya a Shaliz dake yankin Gazne ya hallaka mutane bayan wata motar fashinja ta wuce ta kansa.
Jumazada ya kara da cewa farar hula hudu sun hallaka inda wasu biyu kuma suka jikkata.
Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin akan kowa ba.