Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kaiwa motar 'yan sanda a jihar Pervan da ke kusa da Kabul Babban Birnin Afganistan.
Daraktan 'yan sandan Pervan Abdul Rauf Uruzgani ya shaida cewa, bam din da aka dasa a mahadar hanyar Hufiyan ya fashe lokacin da motar 'yan sandan Pervan ke giftawa.
Uruzgani ya shaida cewa, 'yan sanda 2 tare da direban motar sun rasa rayukansu, wasu mutanen 5 kuma sun jikkata.
An bayyana cewa, wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.