A yankin Afrin da aka kaddamar da Farmakan Reshen Zaitin wanda ke hannun 'yan adawar arewacin Siriya, an tayar da wani bam da aka dasa a cikin wata mota.
Bayanan farko sun bayyana jikkatar mutane 3 sakamakon harin na ta'addanci.
An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitocin yankin, an samu asara a wasu gine-gine.
Jami'an tsaron da suka fara gudanar da bincike sun bayyana akwai yiwuwar 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suka kai harin.