Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Masallacin Juma'a na Wazir Akbar Han da ke Kabul Babban Birnin Afganistan.
An bayyana cewar daya daga cikin wadanda suka mutu shahararren Malamin Addini a Afganistan Muhammad Ayaz Niyazi ne.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin GidaTarik Aryen ya shaida cewar bam din da aka dasa a Masallacin Juma'a na Wazir Akbar Han ya fashe a lokacin Sallar Magriba.
Aryen ya ci gaba da cewar Niyazi tare da wani karin mutum 1 sun rasa rayukansu, sannan wasu karin mutane 2 suka samu raunuka.
Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin tayar da bam din a Masallacin.