Farar hula 1 ya rasa ransa sakamakon harin bam da aka kai a jihar Uruzgan da ke Afganistan.
Kakakin Fadar Gwamnan Uruzgan Zilgey Ibadi ya shaida cewar an binne wani bam a gefen hanya wanda ya tashi a gundumar Chinartu a lokacin da mota duke da fararen hula ta ke wucewa.
Ibadi ya ce farar hula 1 ya mutu sakamakon harin.
Babu wani da ya dauki alhakin kai harin.