Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Afganistan.
Bam din da aka binne a gefen hanya ya fashe a yankin Atai na gundumar Ahmed Abad da ke jihar Paktiya a lokacin da motar fararen hula ke giftawa.
Kakakin fadar gwamnan Paktiya Abdurrahman Mangel ya shaida cewa, fararen hula 5 sun mutu, wasu 4 sun jikkata sakamakon harin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.