Mutane 21 sun samu raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa a kusa da wata makaranta dake jihar Farah din Afganistan.
Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta jihar Farah Abdul Jabbar Shahik ya shaida cewa, a kalla 10 daga cikin wadanda suka jikkata daliban makarantar ne, kuma 3 daga cikin su na cikin halin rai mutu kwakwai.
Shugaban Majalisar Shura ta Farah Dadullah Kani ya shaida cewa, 'yan tawayen taliban sun kai harin bam da bindigu kan cibiyar sojoji da ke gundumar Balabuluk.
Kani ya ce, a arangamar da ta biyo bayan kai harin bangarorin 2 sun yi asarar rayuka, kuma 'yan tawayen sun kama wasu sojoji.
Taliban ba ta fitar da wata sanarwa ba game da batun