Jami'an tsaro 6 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam a cikin wata mota da aka kai a jihar Herat da ke Afganistan.
Gwamnan Herat Sayed Wahid Katali ya shaidawa 'yan jaridu cewa, maharan sun nufi cibiyar jami'an tsaro ta kauyen Kuddus Abad da ke gundumar Kohsan ta jihar.
Shugaban asibitin kasa na Herat ya bayyana mutuwar jami'an tsaro 6, wasu jami'an tsaro 4 kuma sun jikkata sakamakon harin.
Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin