Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke jihar Texas. An fara aiyukan kamo maharan da suka ranta a na kare.
Babu wanda ya mutu ko jikkata sakamakon harin da aka kai sansanin soji na San Antonio-Lackland, an kuma fara gudanar da bincike.
Laftanal Kanal Brian S. Loveless da ke aiki a sansanin soji na Lackland mafi girma a Amurka ya shaida cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka bude wuta a kofar shiga sansanin, ana ci gaba da gudanar da bincike don kamo maharan.
Sakamakon harin an dan rufe kofofin shiga sansanin inda daga baya aka bude su.