Jami'in tsaro 1 ya rasa ransa sakamakon harin da aka kai wa jerin gwanon motocin gwamnan jihar Nuristan da ke Afganistan, Hafiz Abdul Kayyum.
Kayyum da ya fitar da sanarwa bayan kai harin ya bayyana cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai wa jerin gwanon motocin nasa hari a gundumar Surubi a lokacinda suke tafiya daga Nuristan zuwa Kabul Babban Birnin Afganistan.
Kayyum ya kara da cewar jami'in tsaron lafiyarsa 1 ya mutu, wani 1 kuma ya samu raunuka sakamakon harin, amma shi ya kubuta ba tare da samun rauni ba.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.