Mutane 5 sun samu raunuka sakamakon hari da wuka da aka kai a wani babban kanti dake garin Dunedin na kudancin Niyuzelan.
An bayyana cewa, 3 daga cikin wadanda suka jikkata na cikin halin rai mutu kwakwai. An kuma kama maharin.
Firaminista Jacinda Ardern ta shaida cewa, har yanzu ba a san musabbabin kai harin ba.
Ardern ta kara da cewa, 'yan sanda ba su samu dalilan dake nuna harin na da alaka da ta'addanci ba.