An harba makamin roka a kusa da Fadar Shugaban Kasar Afganistan a lokacin da Shugaba Ashraf Gani yake yin Sallar Idi.
An harba a kalla makaman roka 3 zuwa yankin da Fadar Gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama da suka hada da na Amurka suke.
An kai harin a lokacin da Shugaba Ashraf Gani ke gudanar da Sallar Idi.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Mirwais Stanikzai ya shaida cewa,
"Makiya Afganistan sun kai hare-hare a yankunan Kabul daban-daban. Bayanan farko sun bayyana babu wanda ya mutu sakamakon harin."
Bayan harin, Shugaba Gani ya gabatar da jawabinsa.