A garin Irbil na arewacin Iraki an kai hari da makami mai linzami a filin tashi da saukar jiragen sama da sojoji Amurka suke zama. An kashe wutar da ta kama sakamakon kai harin.
Sanarwar da aka fitar daga Sashen Yaki da Ta'addanci na Irbil ta gasgata kai harin.
Akwai sojojin Amurka a sansanin Hariri da aka nufa a harin. An kunna jiniyar karamin ofishin jakadancin Amurka a lokacin da aka kai harin.
Ba za a samu asarar rai ba sakamakon harin, an kuma kashe gobarar da ta kama.
An kara tsaurara matakan tsaro a yankin.