Sojojin Isra'ila da na Hezbollah dake samun goyan bayan Iran sun kwashe sama da shekara guda suna musayar wuta a tsakanin su, yayin da Isra'ilar ta kaddamar da yaki a yankin Gaza saboda harin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktobar bara.
Ma'aikatar lafiyar Lebanon tace hare haren na Isra'ila a Baalbek da Bekaa sun kashe mutane 40 tare da jikkata wasu 53.
Isra'ilar ta kuma bukaci mazauna kudancin Lebanon da su fice daga gidajen su domin bata damar kai hare hare a kan mayakan Hezbollah wadanda ta zarga da kai mata hari da makaman roka.
Tashar talabijin na Al Jadeed tace akalla irin wadannan hare haren sama guda 4 Isra'ilar ta kai yau alhamis a yankin.
Sakatare Janar na kungiyar Hezbollah Naim Qassem yace shi baya tunann ko matakan siyasa na iya kawo karshen wannan yaki da suke fafatawa da Isra'ilar, har sai dole ta daina kai hare haren da take kai wa a yankunan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI