A cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza, tun bayan barkewar yakin a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, hare-haren da Isra'ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutane 46,006 tare da jikkata 109,378.
Sama da mutane 11,000 ne suka bace, wadanda ake kyautata zaton an binne su a karkashin baraguzan ginin da Isra'ila ta kai.
Akalla mutane 30 daga cikin wadanda suka mutu na baya-bayan nan sun faru ne a arewacin Gaza, inda hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaddamarwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 4,000, a cewar hukumomi.
Isra'ila dai na ci gaba da toshe wa kafofin yada labarai na kasa da kasa hanyoyin shiga Gaza.
A tsakiyar Gaza, wani hari ta sama da aka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ya kashe wani uba da ‘ya’yansa uku da sanyin safiyar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa ya bayyana.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wanda ya gabatar da wani jawabi a birnin Paris ranar Laraba, ya ce ana gab da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI