Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 100 a Gaza

Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 100 a Gaza

Jami’an tsaron Civil Defence na yankin Gza sun ce Isra’ila ta yi amfani da makamai masu linzami guda uku wajen afkawa makarantun lamarin da ya kashe tarin mutanen, kuma nan take wasu gawargwakin suka kama da wuta.

Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ba da gan-gan ta kai wannan hari ba, hasali ma ta nufi wani sansanin mayakan Hamas ne, amma kuma harin ya kufce tare da fadawa cikin makarantar Al-Taba’een.

A wata sanarwar ta daban kuma rundunar sojin Isra’ilan ta ce ta sami bayanan sirri da ke nuna cewa mayaƙan Hamas na fakewa cikin fararen hula don samun mafaka a makarantar, shi yasa ta kai harin kan mai uwa da wabi.

Wannan sabon hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wanda dakarun na Isra’ila suka kai cikin wata makarantar ta daban, inda ya kashe mutane 18, harin da Israila ta ce nan ma kuskure ne.

Ƙasar ta Isra’ila ta zafafa a hare-hare a Gaza tun bayan kisan shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a kokarin da take yi na ganin cewa mayaƙan na Hamas basu mayar mata da raddi mai zafi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)