Nasrallah ya caccaki Isra’ilar kan wuce gona da irin ne yayi jwabin da ya gabatar a yau kan fashe-fashen na’urorin sadarwar da aka samu a Lebanon tsakanin ranakun Talata da kuma Larabar makon da muke, lamarin da ya ce sun ƙaddamar da bincike akai.
Jagoran na Hezbolla ya ce ko shakkah babu Isra’ila ta yi wa ƙungiyar tasa illa da hare-haren, sai dai fa ta sani cewar ta riga ta ƙetara duk wata iyaka da suka shata mata, biyo bayan yunƙurin da ta yi na kashe aƙalla mutane dubu 5000 cikin ƙanƙanin lokaci.
Sai dai ya ce wannan barazana ba za ta sa su daina yaƙar Isra’ila ba, har sai ta janye daga yankin Gaza.
Ya zuwa yanzu, aƙalla mutane 37 suka rasa rayukansu, yayin da wasu kusan dubu 3000 suka jikkata a Lebanon, biyo bayan tarwatsewar na’urorin sadarwar na Pagers da Walkie Talkie ko Oba-Oba cikin kwanaki biyun da suka gabata, hare-haren da kai tsaye Hezbollah, Lebanon da kuma Turkiya suka zargi Isra’ila da aiwatar da shi, wadda har yanzu ta ƙi cewa komai akai.
Sai dai rahotanni sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kutsa sarararin samaniyar Beirut,, babban birnin Lebanon, a dai dai lokacin da shugaban ƙungiyar ta Hezbollah Hassan Nasrallah ke gabatar da jawabi ta babbar kafar yaɗa labaran ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI