Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren bam da aka kai a Kabul Babban Birnin Afganistan.
Kakakin Helkwatar 'Yan sandan Kabul Firdaus Faramarz ya shaidawa manema labarai cewa, an kai hare-haren bam a yankunan Pul-i Suhta da Sar Kariz da ke Kabul.
Faramarz ya ce, an kashe mutane 3 tare da jikkata wasu 12 sakamakon hare-haren.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
A 'yan kwanakin nan ana yawan kai hare-hare kan 'yan jaridu, masu fafutuka, Malaman Addini, ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro a Afganistan.
Gwamnatin Afganistan na zargin Taliban da kai hare-haren, amma Taliban na cewa ba ta da alaka da su.