Hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a Iraki

Hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a Iraki

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu kuma wasu 11 sun jikkata a hare-haren da aka kai kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a Iraki.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Cibiyar Sadarwa ta Tsaro ta gwamnatin Iraki ta fitar, an ba da rahoton cewa an kai hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a sassa daban-daban na kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, mutane 7 sun rasa rayukansu kuma wasu mutane 11 sun samu raunuka a wadannan hare-hare.

A cikin sanarwar, ba a bayar da wani bayani game da wadanda suka kai hare-haren kan cibiyoyin samar da wutar lantarkin da kuma irin hare-haren da aka kai ba.

A cikin jaridun cikin gida na Iraki akwai rahotanni da ke cewa an kai hare-hare kan cibiyoyin samar da wutar lantarki a lardunan Mosul, Salahaddin, Diyala da Kirkuk.

An bayyana cewa kungiyar ta'adda ta DAESH na da alhakin kai wasu daga cikin hare-haren.


News Source:   ()