Alkaluma sun nuna cewar harbe-harbe da bindiga da suka afku a birnin New York na Amurka a watan Agustan bana ya ninka wanda suka afku a watan Agustan shekarar da ta gabata.
Sanarwar da sashen 'yan sandan New York ya fitar ta ce a watan Agustan shekarar 2019 an samu kai hari da bindigu sau 91, inda a watan Agustan 2020 kuma aka kai hari da bindiga sau 242.
Daga watan Mayu zuwa yau kuma an kai hari da bindiga sau 791 a birnin, inda aikata muggan laifuka ya karu da kaso 50.
Shugaban New York Bill de Blasio ya bayyana cewar annobar Corona ta yi tasiri sosai wajen yawaitar kai hare-haren.
A garuruwan Amurka da dama ana yawan samun irin wadannan rikice-rikice, a lokacinda ake ci gaba da zanga-zangar adawa da annoba, amfani da karfin da ya wuce ka'ida da 'yan sanda ke yi da nuna wariya.