Hamas ta yi watsi da sharuɗɗan da ke ƙunshe a yarjejeniyar Doha

Hamas ta yi watsi da sharuɗɗan da ke ƙunshe a yarjejeniyar Doha

Wasu daga cikin sharuɗɗan da Hamas ta yi watsi da su a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP sun ƙunshi ci gaba da zaman dakarun Isra’ila a yankin Gaza musamman kan iyakar yankin da Masar, haka zalika batun fitar da wasu fursunonin falasɗinawa ƙetare maimakon basu damar komawa Gaza bayan musayarsu da fursunonin Isra'ilan da ke tsare a hannun Hamas.

Tsawon lokaci aka ɗauka makamanciyar tattaunawar na rushewa tun bayan nasarar tsagaita wutar da aka yi cikin watan Nuwamba, a yakin na fiye da watanni 10 da ya lakume rayukan falasdinawa fiye da dubu 40, baya ga jikkata wasu kusan dubu 100.

A cewar Joe Biden, sakataren wajen Amurkan Antony Blinken zai yi tattaki zuwa Isra’ila a kwanakin ƙarshen makon nan don ganin tattaunawar ta Doha ta samu nasara, ko da ya ke za a ci gaba da makamanciyarta cikin makon gobe a Cairo.

A lokuta da dama da aka ɗauka ana tattaunawar, galibi ko dai Hamas ko kuma Isra’ilan da kanta ke watsi da sharuɗɗan da ke kunshe a yarjejeniyar da ake gab da cimmawa wanda ke kaiwa ga wargajewar zaman.

Sai dai a wannan karon ana ganin Isra’ila da kanta na fatan ganin an cimma yarjejeniyar haka zalika Amurka ta bayayna fatan ganin an kawo ƙarshen yaƙin musamman bayan matsin lamba daga ƙasashen Masar da Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)