Daya daga cikin shugabanin gudanarwar Kungiyar Hamas, Izzet er-Rishk, ya bayyana cewa, a yayin hare-haren da Isra’ila ta kai wa Gaza, Turkiyya ta juya kibiyoyi masu guba na wadanda suka yi biris da laifukan da yahudawan sahayoniya suka aikata.
Da yake bayani a shafinsa na Twitter bayan tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, Rishk ya yi nazarin kasashen da suka tallafa musu yayin hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza.
Rishk ya bayyana cewa, Turkiyya ta dauki tutar Kudus a kan dukkan dandamali na kasa da kasa tare da juya kibiyoyi masu guba na wadanda suka yi kokarin watsi da yin ko oho da laifukan da yahudawan sahyoniya suka yi.
Rishk ya kuma bayyana cewa Qatar da Masar na tattaunawa don dakatar da zubar da jinin al'ummar Falasdinu, yayin da Iran kuma ta tsaya tsayin daka tare da Hamas ta fuskar makamai da kudade.