Wata sanarwar da kungiyar ta gabatar yau bayan fara aiwatar da yarjejeniyar da aka amince da ita, ta jinjinawa jama'ar Falasdinawa saboda jajircewarsu tare da alkawarin sake gina gidajen da suka ce 'yan mamaya sun lalata har zuwa lokacin da zasu kwatarwa yankin 'yancinsa.
Hamas ta ce a cikin kwanaki 471 da aka kwashe ana gwabza yakin, laifuffukan da Isra'ila ta aikata ya gaza kawar da hankalin jama'ar su daga aniyarsu ta bijirewa mamayar yankunansu da ta yi da kuma ci gaba da fitowa domin kare filayensu.
Yankin Gazar ya barke ne sakamakon harin ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023 lokacin da mayakan Hamas suka hallaka akalla Yahudawa 1,210, akasarin su fararen hula tare da garkuwa da wasu daga cikin su.
Isra'ila ta kaddamar da munanan hare haren ramako abinda ya kai ga hallaka mutane kusan dubu 47 da kuma ragargaza gidajen dake Gaza.
Shirin tsagaita wutar kwanaki 42 a matakin farko ya fara aiki jiya da musayar firsinoni daga bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI