Hamas ta sha alwashin baiwa sojojin Isra'ila mamaki bayan rushe tashar kafafen yada labarai
Sojojin Isra’ila sun harbi wani dogon ginar manema labarai a Gaza, wanda ya kunshi ofisoshin kamfanin dillacin labarai na Amurka Associated Press (AP) da kuma ofishin talabijin din Al-Jazeera mallakar kasar Qatar.
An bayyana cewa ginin yana dauke da ofisoshin AP da Al-Jazeera, da ofisoshin likitoci, ofisoshin lauyoyi da kuma gidaje da yawa inda fararen hula ke zaune.
Ginin wanda ke dauke da hasumiyoyin da ke ba da sabis na intanet ga yankuna da dama a Gaza, yana da hawa 13.
Isra'ila a baya ta sanar cewa za a rushe ginin.
Vail al-Dahduh, Wakilin Al-Jazeera na Gaza, ya ce sojojin Isra’ila sun ba mazauna yankin sa’a guda.
A halin da ake ciki, Falasdinawa 10, akasarinsu yara kanana, sun mutu a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani gida a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira na Shati da ke yammacin Gaza, kawo yanzu dai an samu shahidai 139 da kuma 950 da suka jikkata a harin na sojojin Isra’ila tun daga 10 ga watan Mayu kawo yanzu.
Salih al-Aruri, Mataimakin Shugaban Ofishin Siyasa na Hamas, ya ce farmakin da za a fara ta kasa a Gaza zai zama bala'i ga Isra'ila kuma zai sauya daidaiton yakin.
A lokacin da yake magana da gidan talbijin na al-Aqsa na kungiyar Hamas game da labarin cewa Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta kasa a Gaza a jiya, Aruri ya bayyana cewa “dakaru masu jajircewa suna da karfin da za su ba wa makiya (Isra’ila) mamaki kuma suna da makamai masu karfi fiye da makaman da suka yi amfani da su a baya. "