Hamas ta saki Yahudawa guda 3 da ta yi garkuwa da su a Gaza

Hamas ta saki Yahudawa guda 3 da ta yi garkuwa da su a Gaza

Sanarwar rundunar sojin ta ce bayan mika firsinonin guda 3 sun gana da iyayen su, kafin a dauke su zuwa asibiti a tsakiyar kasar.

Rundunar sojin ta gabatar da hotan daya daga cikin su, wato Emily Damari tare da mahaifiyarta lokacin da take murmushi da kuma daga hannun ta wanda aka nade da bandeji.

Wani faifan bidiyon da sojin suka gabatar ya nuna matan 3 lokacin da suke sauka daga motar kungiyar agaji ta Red Cross yayin da ake tarbarsu.

Daga bisani an dauke su a mota zuwa sansanin sojin Reim wanda ke zama sansanin sojin Isra'ila a Gaza inda suka sadu da iyayen su.

Daga nan ne a dauke su da mahaifansu a cikin jirgin saman soji zuwa asibitin Sheba inda sojoji suka yi kawanya domin kare su daga dandazon jama'a.

Ana saran Isra'ila ta fara sakin Falasdinawan da take tsare da su a gidan yari wadanda suka kai 90 a matakin farko.

Tuni motocin agaji dauke da kayan abinci suka fara isa Gaza a karkashin yarjejeniyar da aka kulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)