Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan da ta miƙa wa Isra’ila gawarwakin mutanenta huɗu, a matsayin musayar sakin ƙarin Falasɗinawa 596.
Musayar fursunonin da aka yi cikin daren jiya ita ce ta ƙarshe da aka tsara za ta gudana a ƙarƙashin zangon farko na yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Gaza da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata.
Mutane 25 da kuma gawarwakin ƙarin wasu 8 Hamas ta sakar wa Isra’ila, yayin da ita kuma Isra’ilar ta saki Falasɗinawa kimanin 1,900 ciki har da mata da ƙananan yara, a ƙarƙashin yarjejeniyar da ke daf da ƙarewa.
Har yanzu dai babu wani ƙarin bayani a kan lokacin da ɓangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawa domin ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a zango na biyu, wadda kuma ake sa ran ita ce za ta zama ta dindindin.
To amma a yayin da rashin fara tattaunawar da ake dako ke neman haifar da damuwa, babban jakadan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya ce wakilan Isra’ila na shirin yin tattaki zuwa birnin Doha ko kuma Alƙahira domin fara tattauna wa da wakilan Hamas, tare da masu shiga tsakani na Masar da kuma Qatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI