Hamas ta miƙa wa Isra'ila sunayen mutane 3 da za ta sako mata

Hamas ta miƙa wa Isra'ila sunayen mutane 3 da za ta sako mata

Ofishin Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da karɓar jerin sunayen, sai dai bai bayyana su ga jama’a ba.

Ya zuwa yanzu dai Yahudawa 15 ƙungiyar Hamas ta sakar wa Isra’ila tun bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla a ranar 19 ga watan Janairu nan.

A wani labarin kuma, tsagaita buɗe wutar da aka yi a zirin na Gaza, ya bai wa jami’an ceto damar zaƙulo gawarwaki  354 daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da Isra’ila ta ragargaza.

Wannan na zuwa ne bayan da ma’aikatar lafiyar yankin Falasɗinu ta bayyana ɓacewar mutane fiye da 14,000 a Gazan, yayin da ita kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a iya shafe shekaru aƙalla 20 kafin a kammala kwashe ɓaraguzan dubban gine-ginen da Isra’iila ta rusa a Gaza.

A gefe guda kuma dubban Falasɗinawa ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da  shawarar shugaban Amurka Donald Trump da ya nemi a kwashe al’ummar Gaza baki ɗaya don tsugunar da su a ƙasashen Masar da Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)