A jawabin kakakin rundunar Sojin Isra’ila Rear Admiral Daniel Hagari, ya bayyana cewa nakiya ce ta tarwatsa kwamanda a jiya Lahadi tare da wasu mayaƙansa da suka samu muggan raunuka.
Shi kansa ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant a wani jawabi na daban, ya ce Daksa ya mutu ne lokacin da ya ke yaƙi da Hamas a Jabalia.
Rahotanni sun ce baya ga Daksa akwai kwamanda wata runduna ta daban da shima ya samu muggan raunuka a jiyan sai kuma manyan sojoji da suma suka jikkata.
Zuwa yanzu adadin Soji 358 Isra’ila ta bayyana cewa an kashe mata a Gaza, ko da ya ke wasu bayanan na ganin adadin ka iya zarta wanda ƙasar ke sanarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI