Hamas ta kalubalanaci Google da Apple akan taswirar Falasdin

Hamas ta kalubalanaci Google da Apple akan taswirar Falasdin

Kungiyar Hamas ta kalubalanci kanfunan Amurka da suka hada da Google da Apple akan yadda suke zana taswirar dake nuna bacewar kasar Falasdin abin da ta kira ya sabawa dokar kasa da kasa kuma mataki ne dake nuna banbanci in ji mai magana da yawun kungiyar Hazim Kasim.

"Wannan matakin bangaranci domin goyon bayan Isra'ila ya sabawa ainihin tarihi in ji mai magana da yawun kungiyar Hamas"

Zana taswirar dake nuna shafewar Falasdin karfafa Isra'ila ne kuma lamari ne da ya sabawa doka da ka'idojin kasa da kasa inji mai magana da yawun kungiyar Hamas.

Ministan harkokin wajen Falasdin Riyad el-Maliki ya bayyana cewa tabi'ar kanfunan Google da Apple dake kalubantar kasarsa lamari ne da zasu dauki matakin doka akai.

 


News Source:   www.trt.net.tr