Hamas ta dauki dakaru 15,000 aiki tun bayan fara yakinta da Isra'ila

Hamas ta dauki dakaru 15,000 aiki tun bayan fara yakinta da Isra'ila

Bayanan sirrin na Amurka, sun ci gaba da cewa, duk da dimbin mayakan da Isra’ila ta kashewa Hamas hadi da munanan hare-haren da ta dauki watanni tana kai mata, amma hakan be hanata diban dubban sojojin da za su taimaka mata a fagen daga ba.

Hamas da Isra’ila dai sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Lahadin da ta gabata, bayan kwashe watanni 15 ana yaki, abin da ya jefa yankin Gaza cikin mummunan yanayi.

Sai dai duk da wadannan bayanai, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa har yanzu ofishin daraktan sashen leken asiri na Amurka, yaki amsa tambayoyin da aka gabatar masa.

A ranar 14 ga Janairu ne, aka jiyo tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, na nanata cewa Hamas ta maye gurbin dakarunta da ta rasa a fagen daga, yana mai gargadin cewa kungiyar na ci gaba da samun karfi.

Ko a watan Yulin bara, mai magana da yawun kungiyar ta Hamas, Abu Ubaida, ya bayyana cewa kungiyar na ci gaba da karawa kanta karfi, duk da hare-haren da take samu daga dakarun Isra’ila, yana mai cewa ya zuwa wancan lokacin sun debi dubban mayaka aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)