Wata kungiyar dake fafutukar kare muradun Yahudawa ta bayyana cewar ta samu sunayen wadannan mutane 3 da za'a sake yau lahadi kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.
Mutanen sun hada da Emily Damari da Romi Gonen da kuma Doron Steinbrecher.
An dai kama Damari da Steinbreche a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023 lokacin da mayakan Hamas suka kai samame zuwa kibbutz Kfar Aza, yayin da kuma aka kama Gonen a wajen bikin Nova.
Rahotanni sun ce Isra'ila ta amince ta saki Falasdinawa 50 a kan kowanne Bayahude guda da Hamas za ta sake.
A bangare daya kuma ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar yace za'a ci gaba da samun tashin hankali a Gabas ta Tsakiya muddin Hamas ta ci gaba da mulkin Gaza.
Yayin da yake tsokaci bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla, Saar yace Isra'ila a shirye take ta cimma daukacin kudirorin yakin da ta sanya a gaba, ciki harda tarwatsa gwamnatin Hamas da kuma sojojin ta.
Ministan yace idan kasashen duniya na bukatar dawamammen zaman lafiya a Gaza, ya zama wajibi su bukaci rusa gwamnatin Hamas da kuma rundunar sojin ta.
Saar yace suna iya cimma haka ta hanyar tattaunawa, amma a lokacin tarurrukan da za su yi na gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI