Hamas ta amince ta shiga tattaunawar tsagaita wuta da Isra'ila

Hamas ta amince ta shiga tattaunawar tsagaita wuta da Isra'ila

Sai dai Hamas ta bukaci tattaunawar tsagaita wutar da masu shiga tsakani ke jagoranta ta mayar da hankali kan batutuwan da ta amince da su a baya maimakon fara tattauna sabbi.

Amincewar ƙungiyar ta Hamas domin ci gaba da tattauna batun tsagaita wutar na zuwa ne bayan da Isra’ila ta yi luguden wuta tare da hallaka Falasɗinawa 19 a wasu hare-hare da ta kai ta sama.

Ƙasar Amurka ta ce za’a ci gaba da tattaunawa ranar Alhamis mai zuwa kamar yadda aka tsara kuma ana sa ran cimma matsaya domin tsagaita wuta.

Wata kafar internet a Amurka Axios, ta rawaito sakataran harkokin wajen ƙasar Anotony Blinken na cewa shirye-shirye sun kammala domin tattaunawa a Qatar da Masar da Isra’ila

Gwamnatin Isra’ila ta ce zata tura wakilai domin tattaunawa ita kuwa kungiyar Hamas ta bukaci a mayar da hankali kan batutuwan da ta amince da su tun a baya.

Isra’ila dai ta hallaka Falasɗinawa 19 a wasu hare-hare da ta kai ta sama a yankunan Deir Al-Balah da sansanin Al-Bureij da Al-Maghazi da yankin Rafah

Rahotanni na tabbatar da cewa wannan yaƙin da aka share watanni 10 ana gwabzawa tsakanin Isra’ila da Haamas yayi sanadin mutuwar Falasdinawa dubu 40 ita kuwa Isra’ila ta ce sojojinta 300 ne  suka baƙunci lahira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)